Duk wani matashi dayake takara ajahar Zamfara idan har ya hada hotonsa ko ince poster dinshi da hoton wani tsohon gwamna inabawa Matasan jahar Zamfara Shawara kada su goyamasa baya.
Ubaidullah Yahaya Kaura
Abun mamaki mune matasa mukace mungaji da mulkin da wadannan mutane sukeyimana shekara da shekaru sun dannemu sun hanamu sakat sunkasa inganta rayuwarmu. Mukayi gwagwarmaya domin arage shekarun takara domin mushiga mu kawo Chanji. Amma wai sai kaga dan takara matashi yafito takara kuma ya dauko hoton wani tsohon gwamna wanda bama Zone dinsu gudaba, kuma batakarar gwamna ya keyiba wai Amma ya hada hotonsa dashi wai azabeshi dominshi.
Idan har matashi yayarda da kansa, kuma yasan ciyon kansa kuma yana tare da alummarsa lafiya da girmamamawa baya bukatar sai ya hada hotonsa da wani domin cin Zabe.
Abunda akace shine mugirmama manya, muyi masu biyayya inda suke daidai bawai sai munhada hotunansu danamuba.
Munema kamar yadda suka nema rabo wajen Allah yake. Shiyasa mukace Allah shi zaibamu Alkhairi.
Zaben 2019 na Zuwa yakamata musan ciyon kanmu.